Kulle Masallachin Abdul-Jabbar: Sunusi Ya Yaba Ganduje

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya yaba gami da jinjina ga matakan da gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamnan jihar Ganduje ta dauka na rufe masallacin Abdul-Jabbar Kabara tare da shirya Mukabala Tsakanin shi da Malaman Jihar Kano.

Sunusi II ya yi wannan yabon ne a yayin gabatar da karatun addini da ya saba a gidan shi dake birnin Ikko tarayyar Najeriya.

Tsohon Sarkin ya kara da cewa karatuttukan Abdul-Jabbar sun yi hannun riga da karantarwar addinin Musulunci, kuma ba abu bane wanda za’a lamunci ya cigaba da faruwa, musanman a gari kamar Kano Birni na ilimin addini da martaba manyan bayin Allah.

“Kano muna bisa turba da karantarwar addinin Musulunci ne kamar yadda Shehu Usmanu ?an fodiyo ya ?ora mu akai, bisa ga haka babu wani zindi?i da ya isa ya kawar da jama’armu bisa tafarkin Sunnah ta Annabi da Sahabbansa.

Daga karshe tsohon Sarkin ya bukaci Kanawa da sauran jama’ar Musulmin Najeriya, da su dage wajen sanya Najeriya cikin addu’o’i domin ganin karshen dukkanin matsaloli da fitintinu dake addabar kasar.

Related posts

Leave a Comment