Tsohon Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Buratai, ya bayyana cewa ba abu ne mai sauki ba irin nasarori da ya cimma, ya ce nasarorin da ya cimma sun kai a rubuta kundin littatafai domin yaba masa a aikinsa.
Tukur Buratai, ya ce ya yi rawar gani yayin da yake kan karagarsa a aikin soja, kamar yadda Jaridar TheCable ta ruwaito.
Da yake jawabi ga manema labarai a karshen mako a Abuja, Buratai ya ce akwai “kundi” na nasarorin da ya samu a Hedkwatar Tsaro dake magana kan kokari a aikinsa.
Ya yi magana ne a wani bikin dare da aka shirya wanda mambobin wata kungiya na Kwalejin Tsaro ta Najeriya ta shirya.
Sai dai fadar shugaban kasar ta bayyana nadin nasu a matsayin tukuici saboda aiki tukuru.
