Jiki Magayi: Gwamnoni Sun Gane Kuskure Ne Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Mohammed

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar, Fadar Shugaban kasa ta ce gwamnoni sun gane kuskurensu na yin sulhu da ?an fashin daji masu satar mutane a jihohin arewa maso yammacin ?asar.

Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a wani shirin safe (Good Morning Nigeria) na kafar talabijin ?in NTA na ranar Talata.

Ministan ya ce gwamnoni ba su gane cewa bai kamata su yi sulhu da ?an bindiga ba, inda yanzu suka fahimci kuskurensu.

“Gwamnonin sun koyi darasi daga kura-kuran da suka faru a baya kuma sun yanke shawarar cewa ba za su tattauna da ‘yan fashi ba sai dai su fatattake su,” in ji ministan.

Ya ?ara da cewa yanzu ne gwamnonin suka ?auki matakan da suka dace na magance matsalar ?an bindigar.

A cewar Lai Mohammed, matakan katse hanyoyin sadarwa da hana cin kasuwannin mako da hana sayar da baburan da sayar da man fetur suna aiki a yanzu.

Ya ce an toshe hanyoyi da dama da ke da ala?a da ?an bindigar, musamman katse hanyoyi na mu’amularsu ta samun bayanai da abinci.

Sai dai ministan ya?a labaran na Najeriya wanda ya ce matsalar ?an fashin daji matsala ce da ta shafe tsawon shekaru 10 a Najeriya, ya ce halin da matsalar ta jefa ?asar ba batu ba ne na yanzu.

Lai Mohammed ya ?ora laifin ruruwar matsalar ga rashin shugabanci nagari.

Amma ya yaba wa gwamnonin yankin arewa maso yammaci wa?anda ya ce yanzu sun ha?a kansu domin tunkarar matsalar.

Ministan ya kuma bayyana matsayin gwamnatin Najeriya kan ce-ku-ce-ku-ce da ake kan batun ayyana ?an fashin daji a matsayin ?an ta’adda.

?an majalisar dokokin ?asar ne suka bu?aci gwamnatin Buhari ta ayyana ?an fashin dajin da suka addabi yankin arewa maso yammaci a matsayin ?an ta’adda.

Lai Mohammed ya ce matakan soji da gwamnatin tarayya ke ?auka kan masu aikata laifi ba wai ana bambancewa ba ne tsakanin ?an fashi da ?an ta’adda.

“Mai laifi, mai laifi ne, ko da ?an fashi ne ko ?an ta’adda kuma matakai ?aya ake ?auka akansu.”

“Shi ya sa muke ganin abin dariya ne, kan sukar da ake yi wa gwamnatin tarayya cewa tana yi wa ?an fashi sassauci fiye da ?an a ware da sauran masu aikata laifi.”

“Wannan labaran ?arya ne da ya?a bayanan da ba su dace ba, da wasu masu ya?a labaran ?age da ?arya suke ya?awa,” in ji shi.

Lai Mohammed ya ?ara da cewa “rashin hankali ne ace wa?anda ke kashe sojoji da ?an sanda a ace ana masu sassauci.”

Ya ce tsarin sojoji na ya?i da masu laifi ba ya da wani bambanci tsakanin ?an fashi da sauran masu aikata laifi.

Ministan ya ce sabbin matakan da gwamnonin jihohin da ?an fashi suka addaba suka ?auka na ba sani ba sabo , ana samun nasara.

Ya ce tun farko kamata ya yi a fita a kakkabe su kuma abin da ya faru ya zama darasi a yanzu, domin gwamnoni sun dauki matakan da suka dace.

Related posts

Leave a Comment