Labarin dake shigo mana daga Riyadh babban birnin ?asar Saudiyya na bayyana cewar Sarki Salman na kasar ya bu?aci a gudanar da addu’o’in ro?on ruwa a ranar Litinin.
A sanarwar da ya fitar, ya bu?aci kowa ya tuba ya koma ga Allah da kuma ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi kamar su taimakon jama’a da bayar da sadaka da addu’o’i inda ya ce duka wa?annan sunnoni ne masu ?arfi.
Ma’aikatar harkokin addini ta ?asar ta sanar da daidai lokacin da za a yi addu’o’in inda ta ce minti 15 bayan fitowar rana a duka yankunan ?asar.
