An kashe Shugaban ?asar Haiti Jovenel Moise yayin wani hari da aka kai kan gidansa da ke Port-au-Prince, babban birnin ?asar.
Firaministan ri?on ?warya Claude Joseph ne ya bayyana hakan.
Mista Joseph ya ce wasu ‘yan bindiga ne da ba a san ko su wane ne ba suka afka wa gidan shugaban da ?arfe 1:00 agogon ?asar – 6:00 na safe agogon Najeriya.
Rahotanni sun ce an jikkata matarsa a harin.
“An ?auki dukkan matakin da ya dace na ci gaba da tafiyar da ?asa,” in ji shi.
Jovenel Moïse mai shekara 53 ya hau mulki a Fabarairun 2017 bayan Michel Martelly ya ajiye mu?aminsa.
