Tarbiyya Muke Koyarwa A Hausa Fim – Jaruma Fati Gwammaja


Fitacciyar Jarumar Kannywood Fati Gwammaja wacce aka fi sani da Amina Matar Sambo a cikin shi Kwana Casa’in, ta bayyana hakane a yayin tattaunawa da jaridar dimukura?iyya kan yadda harkar tasu ke tafiya.

“Burina dai shi ne na ga na isar da sakon fadakarwa ta kowanne bangaren, ko ta fim, ko kuma ta murya, domin ina yin wasan kwai-kwayo na rediyo kuma shi ma harkar fadakarwar ce, wajen isar da sako don haka ni, ba ni da wani buri da ya wuce na fadakar da jama’a wajen isar musu da sakon da zan koyar da su tarbiyya, domin ita harkar tana koyar da tarbiyya ne, don haka mu yan fim muna koyar da tarbiyya ne ga Jama’a, kuma muna samun nasara sosai wajen koyar da tarbiyyar. ”

Da aka tambaye ta ko ta taba yin aure?

Sai ta ce” Ka ba ni dariya da ka yi mini wannan tambayar. Ka san ni cikakkiyar Bahaushiya ce, iyaye na ba za su zauna da ni ba su yi mini aure ba. Don haka iyaye na, sun yi mini sutura da dakin miji sun aurar da ni, zama ne dai bai yi dadi ba muka rabu da mijina, kuma bayan auren ya mutu, na sake dawo wa cikin harkar fim. Yanzu dai muna fatan dai Allah ya kawo wanda zai rike ni na zauna a gidan aure Lafiya.

To kenan dai Fati Gwammaja a kasuwa take?

“Haka ne fadi ka kara, ni yanzu a kasuwa nake, ina fatan Allah ya kawo mun miji nagari” a cewar ta

Related posts

Leave a Comment