Ketare: Mutum 12 Sun Mutu A Filin Jirgin Saman Afghanistan


Kungiyar Taliban ta ce mutum 12 ne suka mutu a filin jirgin saman Kabul tun daga ranar Lahadi.

Wani jami’i da ya yi magana da kamfanin dillancin Labarai na Reuters a boye, ya ce mutanen sun mutu ne dalilin turmutsutsu ko kuma an harbe su ne.

Ya bai wa taron mutanen da suka yi dandanzo a filin jirgin shawarar su koma gida tun da ba su da jirgin da zai kai su inda suke so, ya kuma ce “Taliban ba su cutar da ko wa ba a filin jirgin.”

An ta samun rahotannin rikici a filin jirgin lokacin da dubban mutane ke kokarin tsere wa daga kasar.

Har yanzu filin jirgin saman Kabul na karkashin ikon Amurka, sai dai duka titunan yankin a zagaye suke da dakarun Taliban

Related posts

Leave a Comment