Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar wata kotun shari’a da ke zama a Fagge ‘Yan-Alluna a Kano ranar Talata 17 ga watan Agusta ta umarci Halifa Abdullahi da ya share masallacin Juma’ar Fagge na tsawon kwanaki 30 a jere a matsayin hukuncinsa na satan kwafin Alkur’ani mai girma guda takwas.
Malam Abdullahi, mazaunin unguwar Yola da ke cikin birnin Kano, an zarge shi da sata a masallaci a unguwar Tudun Maliki ranar Lahadi da daddare tare da kwashe kwafin Alkur’ani guda takwas.
Sai dai jami’an tsaron masallacin sun cafke wanda ake zargin bayan ya aikata laifin, kuma nan take suka mika shi shi ga ofishin ‘yan sanda na Filin Hockey, wanda a ranar Talata ya gurfanar da shi a kotun Shari’a.
Lokacin da mai gabatar da kara na ‘yan sanda, Abdul Wada, ya karanto tuhumar da ake yi wa Abdullahi, nan da nan ya amsa laifinsa.
Don haka alkalin kotun, Bello Musa-Khalid, ya yanke masa hukuncin share farfajiyar babban masallacin Juma’ar Fagge, na tsawon kwanaki talatin a jere. Rahoto na cewa ana kallon masallacin Juma’a na Fagge a matsayin mafi girma a jihar.
