Jahilci Na Damun Shugabannin Najeriya – Bugaje

An bayyana shugabannin Nigeria a matsayin wanda suka rasa gogewa, da ilmi da ake bu?ata wajen jagorancin ?asa, da ceto ta akan matsalolin ta.

Tsohon ?an Majalisar Nigeria Usman Bugaje ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a Maitama Sule akan wani taro na lekca akan shugabanci, wanda Gamayyar ?ungiyoyin Arewa a Minna, Babban birnin Niger suka shirya.

Bugaje yace sake canje-canje da ake ta nema bashi ne maganin matsalolin Nigeria, inda yace shugabanci nagari ka?ai zai iya magance matsalolin dake fuskantar ?asar, kuma shekaru 20 da akayi ana mulki ya sanya yanzu babu yarda tsakanin Gwamnati da Al’umma.

Yace “shekaru 20 a tsarin Dimokura?iyya, yanayin cin hanci da talauci na ?ara ?arfi. Mun tambayi kanmu, miyasa Dimokura?iyya bata aiki, miyasa ba’a yi mana aikin da muke bu?ata? Ana bu?atar ayi wani abu da gaggawa, bawai maganar wani canje-canje, amma canje-canjen sai da a ?angaren shugabanci.

Tsohon ?an takarar Gwamnan Katsina, ya bu?aci matasa da kada su ka?a kuri’a, da bada goyon baya ga wani ?an siyasa a makance a za?e mai zuwa, inda ya jaddada bukatar dake akwai na’a za?i mutane masu ilmi da gogewa da cancanta.

“Har Shuwagabannin mu basu magance matsalolin tsaro, da talauci da rashin aikin yi, to wannan lokaci ne na canji. Bazamu ta?a bari a kawo mana mutanen da suka kashe ?asa a jami’iyya domin su jagorance mu ba. Jam’iyyun siyasa dole su tabbatar da cewa akwai wasu matakai da zasu za?a wa?anda zasu yi shugabanci,” Inji Bugaje.

Related posts

Leave a Comment