Sukar Gwamnatocin Baya: Atiku Ya Yi Martani Ga Buhari

Tsohon mataimakin Shugaban Kasa, kuma tsohon ?an takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya maida martani ga kalaman Buhari na sukar gwamnatocin baya, inda yace yana alfahari da nasarorin da suka samu a karkashin mulkin Olusegun Obasanjo.

A cikin wata wallafar da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 2 ga watan Oktoba, Atiku ya ce mulkinsu ya biya dukkan bashin da ake bin kasar nan sannan an samu cigaba a fannin tattalin arziki da kashi 6 a kowacce shekara.

“Tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, Najeriya ta biya dukkan bashin da ake bin ta kuma ta cigaba da samun cigaban tattalin arziki da kashi 6. “Wadannan ne lokutan gyara kuma ina matukar alfahari da aiki tare da shugaban kasa Obasanjo da kuma irin ayyukan da muka yi wa kasar nan.”

Tsohon ?an takarar shugabancin kasar ya kara da cewar da akwai gagarumin banbanci a tsakanin salon Mulkin su da na Buhari, inda ya bukaci Buhari da ya zargi gwamnatin shi da ta?arbarewar ?asa, amma ba zargin adalan shugabannin ba wadanda an ga ayyukan su a ?asa.

Related posts

Leave a Comment