Ketare: An Soki Saudiyya Kan Sayen Kungiyar Kwallon Kafa

Rahotanni daga Kasar Saudiyya na bayyana cewar Kar?e ragamar ikon ?ungiyar ?wallon ?afa ta Newcastle da wani kamfanin Saudiyya ya yi a Ingila ya faranta wa mutane da dama amma kuma masu suka da yawa sun yi Allah-wadai da matakin.

Ga wasu dalili shida da suka sa lamarin ya jawo wa babbar ?asa mai tsarki suka.

Gawurtaccen kisan gilla

Kimar Saudiyya ta yi matu?ar fa?uwa game da kisan Jamal Khashoggi a 2018, wani shahararren ?an jarida mazaunin Amurka wanda ya sha sukar gwamnatin ?asar.

Wani lauya mai kare ha??in ?an Adam da Majalisar ?inkin Duniya ta ?auka aiki ya ce wasu ma’aikatan Saudiyya “sun yi gunduwa gunduwa Khashoggi cikin rashin tausayi” a ofishin jakadancin ?asar na birnin Istambul da ke Turkiyya.

Rahoton ya ala?anta Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bn Salman da kisan da kuma wasu manyan shugabannin ?asar. Duk da cewa Yariman ya musanta hannu a kisan, kimarsa ta yi matu?ar zubewa a ?asashen duniya.

Budurwar Jamal Khashoggi, Hatice Cengiz, ta siffanta sayen Newcastle da Saudiyya ta yi a matsayin “abin ?acin rai”.

Mohammed bin Salman ne shugaban gidauniyar Saudiyya wadda ta mallaki kashi 80 cikin 100 na hannun jarin Newcastle, duk da cewa hukumomin Premier League sun ce an ba su tabbacin cewa kulob ?in ba zai kasance ?ar?ashin gwamnatin Saudiyya.

A 2018, hukumomin Saudiyya sun tsare mata 13 masu fafutikar kare ha??i da suka jagoranci kamfe na neman cire haramcin tu?in mota kan mata.

An yi zargin cewa an azabtar da hu?u daga cikinsu sannan masu binciken sun ci zarafinsu.

A 2020, wata kotun musamman kan ta’addanci ta samu wadda ta fi shahara a cikin matan mai suna Loujain al-Hathloul da laifi.

Ta musanta zarge-zargen kuma masu kare ha??i na Majalisar ?inkin Duniya sun bayyana su da “na ?arya”.

Related posts

Leave a Comment