Rahotanni dake shigo mana daga Hedkwatar tsaro ta ?asar Amurka na bayyana cewar gwamnatin kasar ta yi zazzafan gargadi ga gwamnatin tarayya akan amfani da jiragen ya?in da ta sayar mata wajen kai wa ‘yan Bindiga wa?anda ke addabar yankin Arewa maso yamma farmaki.
Tun bayan isowar jiragen Najeriya a watan Yuli bayan kammala ciniki, ?an ?asar da dama sun saka ran cewa nan da nan za a fara amfani da su wajen kai wa ?an fashin daji hare-hare don mur?ushe su, musamman a yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
Sai dai rahotanni sun ce akwai wani babban lamari da ke jawo tsaiko wajen aiwatar da hakan, wanda bai wuce shara?in da ke dabaibaye da sayen jiragen ba tun farko, wanda Amurka ta sanya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Rundunar Sojin Najeriya ta shaida wa Majalisar Dokokin ?asar cewa, tun farko Amurka ta yarda ta sayar da jiragen ya?i na A-29 Super Tucano 12 ne idan za a yi amfani da su a kan ?an ta’adda da masu tayar da ?ayar baya ne kawai, ban da ?an fashin daji.
