An Kakaba Wa Kamfanonin Jiragen ?etare Takunkumi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gwamnatin tarayya ta hana kamfanonin sufurin jiragen sama na ?asashen waje ta?a ku?a?ensu da suka kai dala miliyan 450.

Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa hukumomin Najeriya, ?asar da ta fi saura girman tattalin arziki a Afirka, sun dakatar da fitar da ku?a?en ?asar waje don sayo kaya da kuma na masu zuba jarin da ke son kai wa ?asashensu na asali.

Gwamnati ta ?auki matakin ne saboda ?arancin ku?a?en ?asar waje da ?asar ke fuskanta, musamman na dalar Amurka.

Related posts

Leave a Comment