Rahotanni daga kasar Libya na bayyana cewar Hukumomi a kasar sun bada abin da ya saura na ?asusuwan marigayi tsohon shugaban kasar Muhammad Gaddafi ga iyalansa domin biznewa.
Gaddafi dai ya rasa ransa ne kimanin shekaru 10 da suka gabata a yayin wani kazamin bore da jama’ar ?asar suka yi da sunan kawo sauyi.
Rahotanni sun bayyana cewar an mika kasusuwan Moammar Gadhafi ga danginsa domin sallatarsa, shekaru 10 bayan yi masa kisan gilla tare da binne shi a wani boyayyan waje.
Wannan yana daga cikin mataki na sabuwar hukumar wucin gadin kasar na son wanzar da sulhu a kasar Libiya.
