Kazafi: Tsohon Kwamishina Ya Nemi Afuwar Sheikh Kabiru Gombe

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Bayan barazanar shigar da shi kotu cikin sa’o’i 12 da babban Malami, Sheikh Kabiru Haruna Gombe yayi, tsohon kwamishanan ayyukan Kano ya nemi gafarar Malam.

Muaz Magaji wanda akafi sani da Win-Win Dan Sarauniya ya ce ba shi ya kirkiri labarin ba, a wata jarida ya gani. Saboda haka yana neman afuwar Malam Kabiru Gombe yayi hakuri kada ya gurfanar da shi gaban kuliya.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook. Muaz Magaji yace: “Mallam Kabiru Gombe, sakon Allah wadai da kai kan labarin da na gabatar, ina mai baka hakuri da neman afuwa, kuma ina sanar dakai cewa ba nine na kirkiri labarin ba, Jaridar Punch Hausa ne suka buga shi.

Ina ganin yanzu ka fahimci hakan don naga anja hankalinka ga hakan, wallahi sam bana son Malami ko Sarki na fitar da ra’ayi kururu a siyasa irin tamu ta Nigeria don nasan illar da za ta iyayi mana a addinance da Al’adance, don haka nai sharing labarin don Jan hankali.

Amma in ba kai kayi wannan maganar ba to don Allah kayi hakuri, in kuma ajizan ci yasa kayi to a guji gaba don amana tayi karanci a siyasa.”

Related posts

Leave a Comment