Wasanni: Messi Ya Yi Wa Pele Fintinkau A Cin Kwallaye

Rahotanni sun bayyana cewar shahararren ?an wasan ?wallon ?afa Lionel Messi ya zarce kowa a matsayin ‘dan wasan kwallon kafan nahiyar Amurka ta kudu da ya fi kowa yawan kwallaye a tarihin Duniya.

BBC ta kawo rahoto cewa Lionel Messi ya rubuta sunansa a littafin tarihi bayan ya jagoranci kasarsa ta Argentina zuwa ga nasara a wasan Bolivia.

Sabon ‘dan wasan gaban kungiyar PSG, ne ya zura kwallaye uku a wasan da aka buga a Buenos Aires. Haka ya sa adadin kwallayensa a gida suka kai 79.

Da kwallaye 79 a wasanni 153, Messi ya sha gaban Pele wanda shi ne ke rike da wannan tarihi kafin wasan da aka buga a ranar 9 ga watan Satumba, 2021.

A lokacin da Pele yake buga wa kasar Brazil wasa, ya zura kwallaye 77 a cikin wasanni 92. Pele ya sa wa kasarsa riga ne daga shekarar 1956 zuwa 1970.

Related posts

Leave a Comment