Rahotanni daga Lokoja babban birnin Jihar Kogi na bayyana cewar Gwamnan jihar Yahaya Bello, ya bayyana jihar da yake jagoranta a matsayin wacce tafi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya.
Gwamnan Bello ya fa?i haka ne a yayin da yake jawabi ga mutanen jihar kai tsaye domin murnar cikar jihar Kogi shekaru 30 da kafuwa.
Yace gwamnatinsa ta ?auki lamarin tsaro, ha?in kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali da matukar muhimmanci.
Mun gina Kogi kan tubali mai kyau Bello yace an gina jihar Kogi a kan wasu manyan ginshikai uku, na farko shine toshe duk wata kafa ta handama da babakere da ku?a?en al’umma. Gwamnan ya bayyana sauran ginshikan da kawar da asarar ko batar da ku?a?e ta hanyar da bata dace ba, da kuma ba dukiyar al’ummar muhimmanci wajen tabbatar da duk wata Naira an yi amfani da ita a inda ya dace yadda kowa yake tsammani.
Kogi ta fi kowace jiha zaman lafiya A jawabinsa, Gwamnan Kogi yace: “A halin yanzun babu tantama jihar mu ta fi kowace jiha zaman lafiya a fa?in Najeriya.” “An saka mu a matsayin jiha ta biyu a jerin jihohin da suke cikin zaman lafiya, kuma mu ne na biyu a wa?anda suka fi karancin aikata manyan laifuka.”
