Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya gabatar da kasafin ku?in shekarar 2021 a majalisar dokokin jihar Katsina a ranar Larabar nan.
A jawabinsa na gabatar da kasafin ku?in da aka yi wa taken kasafin farfa?owa da ci gaba, Masari ya ce an shirya kasafin ne ta yadda za a kammala ayyukan da aka fara da kuma samar da wasu sabbi da za a gama kafin wa’adin gwamnati mai ci ya ?are.
Masari ya ce kasafin ya dace ne da bu?atun ?an jihar Katsina, musamman ganin dai da aka tuntu?i ?an jihar su bada tasu gudunmuwar wajen tattara kasafin na ba?i.
Masari ya ce kasafin na ba?i wanda ya tashi kan Naira Biliyan ?282,787,930,655, ya ?unshi manyan ayyuka da za a kashe kashi 70% sai kuma ayyukan yau da kullum da za a kashe wa kashi 30%.
Ku cigaba da kasancewa damu a shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun ruhotanni da dumi dumin su
