Tsohon Shugaban ?asa, Olusegun Obasanjo ya baiyana ?warin gwiwa cewa duk da ?umbin matsalolin da ke damun Nijeriya, komai zai zama tarihi.
Obasanjo ya baiyana hakan ne a wani taron addini na ?an ?ari?ar Deeper Life a birnin Abeokuta a ranar Talata, wanda ya halarta ta yanar gizo.
Obasanjo ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su koma ga Allah domin samun sau?in matsalolin da su ke damun ?asar.
A cewar Obasanjo, duba da irin matsalolin da Nijeriya, Afirka da ma su iya ke ciki, babu abinda mu ke bu?atar sai taimako da ga Ubangiji.
Ya yi kira ga al’umma da su sa imani da Allah a ransu da kuma neman taimakon sa domin Ya yaye matsalolin.
