Karshen Tika-Tika Tik – Shugaban Kasa Ya Sa Wa Dokar Rabon Arzikin Fetur Hannu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Muhammadu Buhari ya sa hannu kan ?udirin Dokar Rabon Arzikin Mai ta ?asa, wanda hakan na nufin ?udirin ya zama doka.

?udirin ya shafe shekaru 10 a gaban Majalisa ana dambarwa da kwan-gaba-kwan-baya a kan sa. Amma a ranar 15 Ga Yuli, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya sa masa hannu, bayan ?udirin ya sha tirjiya da zamiya a majalisun biyu.

Sai dai kuma Buhari ya sa wa ?udirin hannu tare da yin biris da ?orafe-?orafen da al’ummomin da ake ha?o man fetur su ka yi a kan ?udirin.

Al’ummomin dai a ta hannun gwamnonin su da wakilan su da kuma dattijon yankin su na Neja-Delta, Edwin Clark, sun raina kashi 3% bisa 100% na rarar ribas da aka ce za a ri?a warewa domin bun?asa yankunan ta hanyar ilmi da gur?atar yanayi da sauran su.

Su dai al’ummar yankin Neja-Delta sun nemi a ri?a ba su kashi 10% bisa 100%. Ko kuma kashi 5% bisa 100%, kamar yadda Majalisar Tarayya ta amince a lokacin da ta mi?a wa Majalisar Dattawa ?udirin bayan ta kammala aikin ta.

Sai dai kuma a Majalisar Dattawa an zaftare adadin kason da za a ri?a basu, daga kashi 5% zuwa kashi 3% kacal, laamrin da ya tada ?ura sosai a zauren Majalisar.

Idan ba a manta ba, a daidai lokacin da Gwamnonin Neja-Delta da da sauran al’ummar yankin ke ?orafe-?orafe, Ministan Harkokin Neja-Delta Godswill Akpabio, ya ro?i Majalisar Dattawa ta yi biris da ?orafen-?orafen jama’a, ta mi?a wa Buhari ?udirin ya sa hannu, a wuce wurin.

Ministan Harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya shawarci Majalisar Dattawa cewa ta daina tsayawa sauraren ?orafe-?orafen jama’a a kan Kudirin Dokar Raba Ribar Fetur, ta mi?a wa Shugaba Buhari gyaran da su ka yi, shi kuma ya sa hannu ba tare da ?ata lokaci ba.

Ya ce a daina tsayawa sauraren bimbinin al’ummar yankin da ake ha?o fetur, a saki dokar kawai ta fara aiki, a wuce wurin.

Idan ba a manta ba, Dattijo kuma jagoran Yankin Neja Delta Edwin Clerk, ya yi barazanar cewa za su hana ha?o ?anyen mai a Najeriya saboda ?udirin dokar ribar fetur ta fifita wasu jihohin Arewa kan jihohin da ake ha?o mai.

Dattijo mai fa?a a ji a yankin Neja Delta, ya bayyana cewa za su hana kamfanonin ha?o ?anyen mai su ci gaba da aiki a yankin Neja Delta, matsawar dai ba a dawo da kudirin raba ribar man fetur da Majalisa za ta gabatar ba.

Clerk ya ce ‘Yan Majalisar Dattawa da na Tarayya sun raina wa al’ummar Yankin Neja Delta wayau, saboda sun soke kason kashi 10 bisa 100 da za a ri?a ba Neja Delta, su ka maida shi kashi 3 bisa 100, sannan su ka lafta wa wasu jihohin Arewa har kashi 30 bisa 100.

Ya kira wannan ?udiri da cewa, ?udirin iya shege ne da shai?anci da kuma tantagaryar rashin adalci.

“Mu na garga?in cewa jama’ar Neja Delta da an kai su bango. Tutar ta isa haka. Mun gaji da irin mulkin da ake yi mana mai kama da mulkin mallaka, wanda ‘yan uwan mu da abokan mu ‘yan Arewa ke yi mana.

“A yau ragamar harkokin fetur a ?asar nan ta na hannun ‘yan Arewa, duk da dai harkokin ya?i man kamfanonin ?asashen Turai ne ke gudanarwa a madadin Gwamnatin Tarayya.” Inji Clerk.

Dattijo Clerk wanda shi ne jagoran wata ?ungiyar kare muradun Neja Delta, PANDEF, ya ce shi da sauran ?aukacin dukkan ‘yan Neja Delta sun ?i amincewa da kason cikin cokali na kashi 3 bisa 100 na ribar mai da za a ba yankin Neja Delta sa kuma kashi 5 cikin 100 da aka ware wa NNPC Limited da za a rika bai wa al’ummar yankin da ake ha?o man.

“Idan ba a yi mana haka ba kuwa, to ya zama tilas mu tashi tsaye mu fito mu ?waci ha??in mu da tsiya-tsiya. Kuma sai mu hana kamfanonin ha?o ?anyen mai ci gaba da aikin ha?ar mai a yankin mu.”

Shi kuwa Akpabio cewa ya yi “wannan ?udiri da tun shekaru 20 ya ke jibge a Majalisar Tarayya da ta Dattawa. Ina magana ne a madadin jama’ar Neja Delta. Kada fa su jangwalo abin da zai ?ara kawo wa wannan ?udiri cikas. Ko kashi nawa za a ba mu, ko 3, 4 ko biyar kawai mu ha?ura mu kar?a. Daga baya mu koma mu nemi ?ari.”

Related posts

Leave a Comment