Kano: EFCC Ta Gurfanar Da Shahararriyar ‘Yar Damfara Gaban Kotu

Hukumar da ke ya?i da masu yi wa tattalin arzikin ?asa ta’annati, EFCC, reshen Jihar Kano a ranar 16 ga Agusta, 2021, ta gurfanar da Rashida Ibrahim Usman a gaban Mai Shari’a Maryam Ahmed Sabo ta Babbar Kotun Jihar Kano da ke zaune a Milla Road, Bompai, Jihar Kano.

Jami’an Hukumar sun cafke wadda ake zargin ne bayan ?orafin da wata Hajiya Wasila ta yi wanda a cikin watan Afrilun 2018 ‘yar uwarta, Pricia Shaaibu ta gabatar da ita ga wanda ake zargi tare da bayanan cewa ita’ ?ar kasuwa ce mai Ala?a da kasuwanci. Da ake kira Golden Premier Club.

Daga baya, wadda ake zargin ta gayyaci mai ?ara zuwa Abuja inda ta bayyana mata cikakken bayanin kasuwancin. Wanda ya shigar da ?arar ya nuna sha’awar kasuwancin kuma ya sanya jimlar Kudi Naira 13,780,000 (Miliyan Goma sha Ukku, da ?ari Bakwai da Tamanin) an biya ku?in ne ta hanyar asusun wanda ake ?ara wanda ke zaune a bankin Diamond Plc tare da asusun N0. 0099629622.

An karanto ma wadda ake ?ara, “cewa ke Rashida Ibrahim Usman wani lokaci a cikin shekarar 2018 a Kano, a ?ar?ashin ikon wannan Kotun Mai Girma, da nufin yin ha’inci, kun kar?i ku?i Naira Miliyan goma sha uku da dubu ?ari Bakwai da tamanin daga asusun Hajiya Wasila.

Wadda ake tuhumar ta musanta zargin da ake yi ma ta.

Dangane da rokon da ta yi, lauyan masu gabatar da kara, Zarami Muhammad, ya ro?i kotun da ta tsare wadda ake ?ara a gidan yari tare da tsayar da ranar da za a fara shari’ar.

Lauyan da ke kare wacce ake ?arar, Abdullahi Muhammad, ya sanar da kotun cewa ya shigar da Bu?atar neman belin wadda yake karewa, sannan ya bukaci kotun ta amince da belin ta.

Mai shari’a Sabo ya bayar da belin wadda ake tuhuma a kan kudi Naira Miliyan Biyu (N2,000,000) da mutum biyu masu tsaya ma ta.

Wadanda za su tsaya ma ta dole ne su kasance suna da kadarorin da ba za a iya gazawa ba ko kuma kadarorin da suka kai Naira Miliyan Biyar (5,000,000) a cikin Jihar Kano.

An daga shari’ar zuwa ranar 25 ga Oktoba, 2021, domin shari’a.

Related posts

Leave a Comment