‘Yan Siyasa Sun Fi ‘Yan Bindiga Barna – Dr Gumi

Fitaccen malamin addinin musulunci na Najeriya Sheikh Ahmad Gumi ya yi karin haske gami da bayani cikakke kan yadda yake yawan tattaunawa da yan bindiga akai-akai a kasar nan.

Shehin malamin dan jihar Kaduna ya ce, sau dubu gwamma yan bindiga da wasu yan siyasar kasar nan akan rashin tabukawa al’umma komai da yiwa matsalar rashin zaman lafiya zagon kasa.

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewar, wasu fitattun yan siyasar Najeriya ne ke masa zagon kasa a kokarin sa na tattaunawa da yan ta’adda don ganin an sami tsaro.

Babban malamin dan asalin jihar Kaduna a arewacin Najeriya ya bayyana cewar, babu wata rawa da wasu yan siyasar kasar nan kan taka gameda matsalar rashin tsaron da ake fuskanta. Amma kuma suna yiwa masu kokarin kawo zaman lafiya zagon kasa.

Sheikh Ahmad Gumi babban malamin addinin musulunci wanda ya shahara da shiga dazuka don tattaunawa da yan bindiga don kawo zaman lafiya a kasar ya ce, “muddin gwamnati bata jinjina masa kan kokarin sa ba, To bai kamata a kushe aikin na sa ba”

Jaridar Sokoto

Related posts

Leave a Comment