Kano: Muhuyi Rimin Gado Ya Ki Bayyana Gaban Majalisa

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Majalisar dokokin jihar ta dakatar da bincikar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado, dakataccen shugaban hukumar karbar korafi da yaki da rashawa ta jihar Kano.

Kwamitin wucin-gadi na majalisar a wata takarda da suka fitar a farkon makon nan, sun bukaci Rimin Gado da ya bayyana a gaban majalisar da karfe 12 na ranar Laraba, domin amsa tambayoyi.

Amma kuma a yayin jawabi ga manema labarai bayan bayyanarsa a gaban majalisar, sakataren kwamitin wucin-gadin, Abdullahi A. Bature ya ce zaman ba zai cigaba ba saboda kwamitin sun kafa tsarin bincikar Rimin Gado kamar yadda wasikar lauyansa ta bukata a ranar Laraba.

Bature wanda shine mataimakin daraktan shari’a na majalisar, yayi bayanin cewa Rimin Gado ya ce ba zai iya halartar zaman ba saboda rashin lafiya kuma sun bukaci takardu kuma za a basu.

A zama na gaba, Bature ya ce kwamitin zai yi martani kan wasikar da Rimin Gado ya aiko musu kuma za a mika musu gayyata idan akwai bukatar hakan.

Lauyan Rimin Gado, Usman Umar Fari, ya tabbatar da cewa wanda yake karewa bai samu damar zuwa ba saboda bashi da lafiya kuma suna bukatar dukkan abubuwan da zasu yi amfani dasu wurin bashi kariya.

“An dakatar da Magaji a ranar 5 ga watan Yuli kuma babu wata takarda da aka mika masa ta hakan har yau, ba a bashi takardar dakatarwa ba kuma ba a bashi kwafin zargin da ake masa ba.

“Takardar da muka samu ita ce wasika mai kwanan wata 12 ga Yuli wacce ke gayyatarsa gaban kwamiti ba tare da an saka sunansa ba balle na mai kara ko kuma zargin da ake masa,” .

Related posts

Leave a Comment