Hukumomin Saudiyya sun ce za su tura wasu mutum-mutumai cikin masallacin Harami domin su rika raba ruwan zam-zam ga maniyyata aikin Hajjin bana.
Wata sanarwa da shafin Haramain da ke kula da masallacin Haramin ya wallafa a Tuwita ta ce manufar yin hakan ita ce a kauce wa kamuwa da cutar korona.
“Hukumar Haramain tana shirin tura mutum-mutumai da zummar gogewa da kuma raba ruwan Zamzam ga masu aikin ibada a masallacin Haramin, lamarin da ya yi daidai da shirin shugabanni na karbar mahajjata na shekarar 2021,” in ji sanarwar.
Da ma dai hukumomin kasar sun bayyana cewa mutum 60,000 ne za su gudanar da aikin hajjin bana, kuma za su kasance mazauna kasar ta Saudiyya.
