Kano: Mahaukaciyar Gobara Ta Yi Barna A Hukumar SEMA

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar wata Mahaukaciyar Gobara da ta tashi ranar Jumu’a da yamma a siton hukumar kai agajin gaggaywa SEMA ta lakume kayayyakin da suka kai darajar miliyan N18 da rabi.

An ruwaito cewa wutar ta yi wannan aika-aika ne a Siton SEMA dake Mariri, ?aramar hukumar Kumbutso dake jihar Kano.

Sakataren hukumar SEMA, Dakta Saleh Jili, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin hira da manema labarai a Kano ranar Jumu’a.

Ya ce lamarin ya auku ranar Jumu’a da karfe 1:00 na rana a Siton Mariri, wurin da ake aje kayayyakin taimakon wanda lamarin gobara ya shafa da ambaliyar ruwa.

Abubuwan da wutar ta cinye sun ha?a da tabarmu 450, matashi 450, abun yin nafkin na yara da manya katan 655. Sauran kayayyakin sun ha?a da Katan ?in Dettol 10, Kekunan ?inki. da na aikin wuta, ragar sauro da sauran abubuwa, da suka kai kudi Miliyan N18.5m.

Yace: “Jami’an mu zasu tantance asarar da aka yi da kuma darajarsu domin mi?a wa shugabannin mu na gwamnati.” Bayan haka kuma, ya yi kira ga al’umma su yi taka tsantsan da wutar daji domin kiyaye kayan su da kuma lafiyar su.

Related posts

Leave a Comment