Siyasantar Da Zanga-Zanga: Tinubu Bai Damu Da Halin Da ‘Yan Kasa Ke Ciki Ba – NLC

IMG 20240226 WA0252

Kalaman na baya-bayan nan da aka danganta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a lokacin kaddamar da aikin layin dogo na Red-Line Railway Project ya haifar da damuwa matuka a cikin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC.

Muna ganin wa?annan kalamai, Musamman wadanda suka shafi rawar da kungiyar kwadago ke takawa wajen gudanar da mulki, suna da banbanci sosai da gwagwarmayar da talakawan Najeriya ke fuskanta a ?ar?ashin manufofin da ake da su.

Maganar da Shugaba Tinubu ya yi na cewa Labour ba ta da ginshi?in ?alubalantar Gwamnatinsa, watanni tara kacal a kan karagar mulki, abin damuwa ne sosai. Bugu da kari, mayar da hankali kan batutuwan bangaranci da kuma zabukan 2027 mai nisa, maimakon bukatun gaggawa na jama’a, yana kara nuna rashin alaka da halin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a kullum.

Abin takaici ne yadda Shugaban kasar ya ya nuna Bai damu da irin wahalhalun da miliyoyin ‘yan Nijeriya suke ciki ba. Yunwa rashin aikin yi, Rashin tsaro, Hauhawar farashin kayan Masarufi. kiwon lafiya na bu?atar kulawa cikin gaggawa da ?aukar matakin gaggawa. Amma duk da haka, maimakon magance wadannan matsalolin da ke damun Yan ?asa

NLC na son jaddada cewa babban burinmu shi ne kada mu nemi mukamai na siyasa, ciki har da na Shugaban kasa. Maimakon haka, abin da muka fi mayar da hankali a kai shi ne bayar da shawarwari don samar da ingantaccen Shugabanci wanda ya ba da fifiko ga walwala da tsaron dukkan ‘yan Nijeriya. Muna kira ga shugaba Tinubu da ya karkato da kokarinsa wajen ganin ya cika wannan muhimmin aikin da ya rataya a wuyan Gwamnati, a maimakon yin kalaman siyasa.

Ya zama wajibi mu sake mayar da hankali kan makamashin hadin gwiwarmu wajen tunkarar muhimman batutuwan da suka kasance batun kulla alaka tsakanin kwadago da gwamnati tun daga watan Yunin 2023. Wa?annan sun hada da muhimman batutuwa kamar karin albashi, shirye-shiryen jin dadin jama’a, samar da ababen more rayuwa, da farfado da harkokin kasuwanci. muhimman sassa kamar ilimi da kiwon lafiya.

A kowanne hali Yana da mahimmanci mu mayar da hankali kan ainihin batutuwan saboda mun shiga cikin Gwamnati tun watan Yuni 2023 bayan An Cire Tallafin man fetur. Batutuwan dai sun shafi rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin mu da Gwamnati. Inji Kungiyar Kwadago

Ya mai girma shugaban kasa, an cimma wa?annan yarjejeniyoyin amma kwamitin da aka ?orawa alhakin gudanar da wadannan ayyuka ba a taba kaddamar da su ba, kuma ba a aiwatar da ko daya daga cikinsu ba, sai da aka tilasta mana shirya wani gangami a fadin kasar, yayin da shugaban kasa ya bayar da himma. Sai dai mai girma shugaban kasa, babu abin da ya fito daga alkawuran da ka dauka.

An dauki wani zagaye na zanga-zangar don cimma yarjejeniyar Ranar 2 ga Oktoba, 2023. Mun zayyana yarjejeniyar a kasa Domin Gwamnatin ka ta fada wa ‘yan Najeriya wacce ta iya aiwatarwa. Su ne;

1. Abu na farko a cikin yarjejeniyar shine Palliative N35,000.

2. Matatar Port Harcourt za ta fara aiki a watan Disamba, 2023.

3. Za a aiwatar da tallafin kudi 25,000 ga talakawa miliyan 15.

4. Tauye haraji ga ma’aikata, ?ananan ‘yan kasuwa da sauran jama’a.

Related posts

Leave a Comment