Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar a ranar yau Jumu’a Kotun ?oli zata yanke hukunci kan ?arar da aka gabatar gabanta game da rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyyar APC reshen jihar Kano.
An ruwaito cewa jam’iyyar ta tsage gida biyu tsakanin tsagin dake goyon bayan gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Ganduje, da tsagin yan G-7 karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau.
Masu shigar da ?arar wa?anda ke tsagin G-7 su suka fara samun nasara a babbar Kotu, amma tun ba’a je ko ina ba Kotun ?aukaka ?ara ta warware hukuncin ta ba tsagin Ganduje nasara.
Rashin gamsuwa da lamarin ya sanya ?angaren masu shigar da ?ara suka garzaya Kotun ?arshe a ?asar nan suka bukaci ta jingine hukuncin baya. Sai dai tsagin Gwamna Ganduje na ganin cewa zuwa Kotun koli da suka yi ba wani sabon abu bane idan mutun ya ?auki matakin haka.
Bayan jin ta bakin kowane ?angare a ranar 8 ga watan Afrilu, Kwamitin al?alai 5 da ke jagorantar shari’ar bisa jagorancin Mai Shari’a Mary Peter-Odili, ta ?age sauraron hukuncin zuwa ranar yau juma’a 6 ga watan Mayun 2022.
