Borno: Zulum Ya Sauke Dukkanin Kwamishinoni

Rahotannin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya sauke dukkanin kwamishinoninsa daga mukamansu.

Wannan lamarin ya auku ne a ranar jiya Alhamis, 5 ga watan Maris 2022 inda ya sanar da hakan a wata takarda da gwamnan ya fitar a shafinsa na Facebook da Twitter.

A cewar gwamnan, ya yi hakan ne domin bai wa duk masu burin tsayawa takarar wata kujerar siyasa fitowa su tsaya ba tare da sun karya doka ba.

Sallamar kwamishinonin wanda ya fara aiki nan take, yana kunshe ne cikin takardar da babban sakataren gudanarwa, Danjuma Ali, yasa hannu a madadin sakataren gwamnatin jihar.

An umarci dukkanin kwamishinonin da su mika lamurran ma’aikatunsu hannun manyan sakatarorin ma’aikatun.

Zulum ya bayyana godiyarsa ga mambobin majalisar zartarwan kan gagarumar gudumuwar da suka bayar yayin da suke rike da ofisoshinsu kuma yayi musu fatan alheri a nan gaba.

Related posts

Leave a Comment