?asar Amurka ta sanar da shirin tallafawa Najeriya cikin gaggawa da dala miliyan 55 domin taimaka wa ?asar wajen shawo kan matsalar tsada da ?arancin abinci.
Wannan wani ?angaren ne na alkawarin Shugaba Joe Biden a taron G7 da aka gudanar a Jamus, a ?o?arin ceto ko kare matalautan ?asashen daga matsalar abinci da ke addabar duniya sakamakon mamayar Rasha a Ukraine.
Amurka ta sanar da wannan shiri ne a wata sanarwa da ofishin jakadancinta a Najeriya ya fitar, inda take cewa wa?annan ku?a?e za a bayar da su ne ta hannun Hukumar raya ?asashe ta Amurka, wato USAID ?ar?ashin shirinta na noma, ciyarwa da taimakon agaji.
Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, a cikin sanarwar tana cewa ku?a?en za su taimaka wajen shawo kan matsalolin tattalin arziki, wadatuwar abinci da abinci mai gini jiki a yankunan da mutane ke fama da talauci a Najeriya, da kuma tsadar rayuwa da ke sake taggayara al‘ummarta.
Mary Beth Leonard, ta kuma sake jaddada munufofin Amurka da al’ummarta domin inganta tattalin arzikin ?ai?aikun mutane da sama musu abinci wadatacce a Najeriya.
