Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar wakilai ta nuna alhininta a kan yadda wasu bangarorin gwamnati suke adana kudin shigarsu da suke tarawa suna barin gwamnatin tarayya da nemo bashin kudin kasafi.
An ruwaito yadda majalisar ta soki yadda gwamnati ta ketara kasar waje don cin bashin naira tiriliyan 5.62 don cikasa kasafin shekarar 2022, yayin da wadannan bangarorin gwamnatin suke killace kudaden a asusansu.
Honorabul James Faleke, shugaban kwamitin majalisar a fannin kudade ya bayyana hakan ne a wani taro na sauraron bayanan rahoton MTEF da FSP na shekarar 2022 zuwa 2024 a ranar Alhamis a Abuja.
Ba mu ji dadin yadda Najeriya take narkar bashin naira tiriliyan 5.62 ba kuma yanzu haka akwai kudade a kasa wadanda ba a riga an yi amfani dasu ba. Tsakani da Allah ya kamata mu gina kasar nan tare ne saboda mu amfana,” a cewarsa.
Faleke yace babban matsalar da muke fuskanta a kasar nan shine samar da kudaden shiga, inda ya kara da cewa majalisar wakilai za ta fi son ta ji nawa ma’aikatu suke tarawa, a asusun Ma’aikatun nasu.
A cewarsa, matsawar majalisar wakilai ta gano cewa akwai wata ma’aikata ta gwamnati wacce ba dole bane aikinta, za a cire ta don sassautawa kasafin kasa.
Kwamitin ya bukaci NCC da ta samar da bayanin yawan kudaden da aka samu daga dukkan kamfanonin sadarwa tun daga 2018 zuwa 2020.
