Babbar kotun jihar Kano Mai Lamba biyar ?ar?ashin jagorancin Mai Shari’a A’isha Mahmud ta bada umarnin a kamo mata mawa?i Ado Isa Gwanja.
An rawaito Kotun ta kuma haramta masa wa?a har sai ‘yan sanda sun kammala bincike a kansa.
Idan za’a iya tunawa a bara lokacin da mawa?in yayi wata wa?a mai suna “WAR” zauran malaman Kano sun shigar da shi ?ara a kotun Shari’ar Musulunci dake Bichi ta hannun lauya Barr. Sulaiman Gandu, saboda a cewar su wa?ar akwai kalaman batsa a cikinta kuma zata iya ?ata tarbiyyar yara a Kano.
A wancan lokacin kotun ta bada izini a kamo mawa?i ado Gwanja, amma sai ya garzaya babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba biyar ya kuma kar?o takardar da ta hana kotun ta kama shi a wancan lokacin.
A zaman ta na wannan rana kotun ?ar?ashin jagorancin mai Shari’a A’isha Mahmoud ta bada umarnin a kama Ado Gwanja, sannan ta ce ta haramta masa yin kowacce irin wa?a har sai ‘yan sanda sun kammala bincike kan zargin da malaman Kano suka yi masa.
Haka zalika kotun ta ce ta haramtawa Ado Gwanja zuwa gidan biki don yin wa?a, sannan kuma ta hana wani ko wata ya hau wakar sa a dandalin sada zumunta.
Kotun ta ce duk wanda ya hau wa?ar kafin a kammala wannan Shari’ar to su sani sun karya doka kuma kotu zata sa a Kamo su.
