Rundunar ?ansandan Najeriya ta ce za ta bai wa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a ?asar kariya, sai dai ta ce za ta ?auki duk wasu matakan hana ?arkewar rikici.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, kwana?aya kafin zanga-zangar tsadar rayuwa da ?ungiyar ?wadago ta ?asar (NLC) ta kira a fa?in ?asar.
A cikin sanarwar wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar ?ansandar ta ?asa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ta ce “Rundunar ?ansanda na sane da ?ancin da al’umma ke da shi na yin zanga-zanga cikin lumana kamar yadda doka ta tanada.”
Sai dai rundunar ta ce “yayin da take martaba ?ancin yin zanga-zanga cikin lumana, rundunar ?ansandan ta Najeriya ta ce za ta sanya ido kan duk wanda ya shiga zanga-zangar da mummunar manufa.”
“Sabida haka, rundunar ta ce ba za ta ?ata lokaci ba wajen mur?ushe su ta duk hanyar da ba ta sa?a wa doka ba.”
