Kungiyar Kwadago Ta Dakatar Da Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa

FB IMG 1709098029346~2

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta sanar da dakatar da zanga-zangar da ta shiga na kwanaki biyu a fadin kasar, domin nuna adawa da manufofin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu.

A karshen taronsu na ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, kungiyar ta shaida wa manema labarai cewa an cimma manufar gudanar da zanga-zangar ne a ranar farko da fara ta zanga-zanga.

Sanarwar da shugaban kungiyar ya fitar na cewa: “Saboda haka, taron NEC ya yanke shawarar dakatar da zanga-zangar a rana ta biyu bayan da aka samu gagarumar nasara, don haka an cimma mahimman manufofin zanga-zangar na kwanaki 2 a ranar farko.”

Kungiyar ta kuma yaba ma daukacin ‘yan Najeriya, shugabanni da ma’aikata kan tururwa da suka yi a fadin kasar don yin zanga-zangar lumana kan halin da ake ciki.

An shirya zanga-zangar ne sakamakon cire tallafin man fetur wanda ya janyo hauhawar farashin kayan abinci, tabarbarewar tattalin arziki, hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa a kasar.

Related posts

Leave a Comment