Gwamnatin Tarayya ta bayyana raba kwanukan cin abinci har guda miliyan 1.2 ga makarantun firamare a Kano.
Wannan shiri dai an ?ullo da shi ne domin inganta matakan tsaftace abincin da ‘yan makarantar ke ci da kuma nuna kulawa da lafiyar su.
Ministar Harkokin Agaji, Jin?ai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Faruk ce ta bayyana haka, a lokacin fara rabon kwanukan da aka yi a Makarantar Firamare ta ?walli, wadda ke cikin birnin Kano.
Bashir Al?ali, Babban Sakatare na Ma’aikatar Jin?ai ne ya wakilci Minista Sadiya, a wurin fara rabon kayan, a ranar Laraba a Kano.
Shirin dai ya na gudana a ?ar?ashin Shirin Ciyar da ‘Yan Makaranta na Gwamnatin Tarayya, wato NHGSFP.
Sadiya ta bayyana cewa shirin wani ha??asa ne da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi na raba kwanukan cin abinci ga ‘yan firamare a jihar Kano.
“Shirin HGSFP dai shiri ne na bayar da tallafi ga marasa galihu a ?ar?ashin NSIP, da nufin ?ara yawan ?aukar ?ananan yara makarantun firamare, tare da inganta ba su abinci mai gina jiki.” Inji Al?ali.
Minista Sadiya ta ce zuwa yanzu gwamnati ta ciyar da yara ‘yan makaranta har miliyan 9, kuma ta ?auki hayar mata masu dafa abinci har 100,000 a fa?in ?asar nan.
Ta ce jama’a da yawa sun samu damar samun ayyukan yi a ?ar?ashin shirin ciyar da ?alibai.
Tun da farko Gwamna Abdullahi Ganduje ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da Minista Sadiya Faruk, bisa ?o?arin su na ganin ?aliban Jihar Kano sun samu abinci mai gina jiki.
