Hukumar za?e mai zaman kanta ta ?asa INEC ta bayyana cewar ko ka?an ba za ta ?ara wa’adin da ta dibar wa jam’iyyun siyasa na su gudanar da za?en fidda gwani ba domin tunkarar babban za?e dake tafe na shekarar 2023.
A cikin jadawalin da INEC ta fitar na shirye-shiryen za?en 2023, hukumar ta ware tun daga ranar 4 Ga Afrilu zuwa 3 Ga Yuni ya kasance tilas kowace jam’iyya ta gudanar da za?en fidda-gwani, kuma ta fitar da ?an takarar kowane mu?ami a jiha da ?asa baki ?aya.
Ana sauran kwanaki 28 kenan wa’adin fitar da ?an takara ya cika, APC da PDP sun nuna ba su shirya gudanar da za?ukan fidda gwani ba.
Yayin da APC har yanzu ta na ci gaba da sayar da fam na takara, ita kuwa PDP yanzu ne ma ta ke tantance wa?anda su ka nuna sha’awar tsayawa takarar.
Sai dai kuma rahotanni na nuni da cewa manyan jam’iyyun biyu su na ta neman kamun-?afar INEC domin a ?ara masu lokaci.
