Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar kimanin mutum sama da 200 ne suka kamu da cutar amai da gudawa a ?auyuka 16 da ke yankin karamar hukumar Rano a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Hukumomi a yankin karamar hukumar Rano sun ala?anta bullar cutar da gur?atacen ruwan sha da rashin tsaftar muhalli.
A makwannin da suka gabata ne dai Ma’aikatar Lafiya a Kano ta ce daga watan Maris zuwa watan Yunin da ya gabata mutum sama da dubu uku ne suka kamu da cutar amai da gudawa a jihar, kuma mutum 100 daga cikinsu sun mutu.
Faruwar wannan al’amari dai na nuni da cewar duk da matakan da ma’aikatar lafiya ke cewar ta dauka kan cutar ta amai da guda, a iya cewa al’amarin na ci gaba da fantsama zuwa karin wasu kananan hukumomin baya ga 33 da ta ce an sami cutar a watanin da suka gabata.
