Kano: Ban San Dalilin Kamani Ba – Rimin Gado

Tsohon shugaban hukumar ya?i da cin hanci ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya tabbatar wa BBC Hausa kama shi da ?an sanda su ka yi amma ya ce ba a fa?a masa laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

?an sanda sun kama tshohon shugaban ne wanda ke neman tsayawa takarar gwamnan Kano a babban za?e na 2023 a Abuja yayin da ya je aikin tantancewa da jam’iyyar PDP ta shirya.

“Babu wanda ya fa?a min dalilin da ya sa aka kama ni, ba a fa?i wani laifi ba a takardar izinin kama ni,” in ji Muhuyi cikin wani sa?o da ya aike wa BBC.

Wata takarda da aka gabatar wa Muhuyi ta nuna yadda wata kotun majistare a Kano ta ba da umarnin kama shi.

Yanzu haka yana tsare a ofishin ‘yan sanda na Abuja, babban birnin Najeriya.

Gwamnatin Kano ?ar?shin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da Muhuyi ne daga mu?aminsa bayan zargin sa da bada?ala a wasu kwangiloli da kuma aringizo tare da ?addamar da bincike kan sa a watan Yulin 2021.

Related posts

Leave a Comment