Shugaban hukumar ya?i da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ya tabbatar da cewa ba za su bar manyan ?arayi ba a ya?in da suke yi da masu ala?a da cin hanci da rashawa a ?asar.
Mista Ola Olukoyede ya ce ba za su bar kowa ba a aikin da suke yi. Ya ce a daidai lokacin da suke bin manyan ?arayi, za kuma su ci gaba da bin sawun ?ananan ?arayi.
Ya ce aikin da EFCC take yi zai ci gaba da kara?e ko’ina, da kuma kan kowa da kowa ba tare da wani da ke ala?a da duk wani nau’in laifin ku?i ko na tattalin arzi?i ya ku?uta ba.
Shugaban na EFCC ya ba da wannan tabbaci ne ranar Lahadi lokacin da hukumarsa ta shirya wani taron wayar da kai da kuma yun?urin shigar da jama’a cikin harkokin ya?i da cin hanci da rashawa.
A cewarsa, a cikin wata biyun da ya wuce, hukumarsa ta EFCC ta gurfanar da tsoffin gwamnoni guda biyu gaban shari’a.
Ana dai sukar hukumar ta EFCC da cewa ta zama kyanwar lami, ba ta iya bin manyan ‘yan siyasa da sauran manyan masu ri?e da mu?aman gwamnati wa?anda ake zargi da tafka gagarumar sata da kuma almundahana da dukiyar al’umma.
Sai dai, Mista Ola Olukoyede ya ce ba gaskiya ba ne a ce EFCC ta fi kauri wajen kama masu damfarar intanet.
