Aikin Gama Ya Gama: Ba Za Mu Kara Wa’adin Rijistar Katin Zabe Ba – INEC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta ?asa INEC ta ce ba zata sake bude kofar mallakar katin zabe ba ga yan kasar, bayan cikar wa’adin ranar 31 ga watan Yulin 2022.

Kwamishinan Hukumar mai kula da sashen ilmantar da al’umma kan mallakar katin, Festus Okoye, ya fada wa BBC cewa sun bai wa jama’a duk irin lokacin da suke bukata don mallakar katin.

Akan haka yace ba za su sake tsawaita lokacin yankar rajistar ba, lura da yadda lokaci ke kure musu.

INEC ta ce tana so ta mayar da hankali ne ga sauran ayyukan da ke kan jadawalin zaben na 2023, kuma dole sai ta rufe yankar katin ne za ta iya samun ci gaba.

A ranar 28 ga watan Yuni ne hukumar zaben ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar zuwa ranar 31 ga watan Yulin 2022, bayan bukatar hakan daga bangarori daban-daban na kasar.

Related posts

Leave a Comment