Kano: An Yi Zanga-Zangar Adawa Da Sace-Sacen Yara

Iyayen yara mata da dama ne da yaransu suka bace, suka gudanar da zanga-zanga a jihar Kano, don nuna bacin ran su kan abun da suka kira halin ko in kula da hukumomi ke nuna wa wajen ganin an nemo yaransu.

Matan, wadanda ke rike da kwalaye da ke dauke da rubutu da hotunan yaran da suka bata, sun je hukumar karbar koken jama’a ta jihar da kuma Ma’aikatar Harkokin Mata domin mika bukatarsu.

A dukkan wuraren, shugabar tawagar Zainab Abdullahi Giginyu, ta ce abun da ya dake su shi ne, tsawon shekaru suna ?orafi kan batun amma har yanzu gwamnati ta ki yin abun da ya dace.

Da suke jawabi ga masu zanga-zangar, Kwamishinan Harkokin Matan jihar Zahara’u Muhammad da kuma Shugaban hukumar sauraron koken jama’ar Barrister Muhuyi Rimin Gado, sun ba matan tabbacin gwamnatin jihar, na yin duk abun da za ta iya, na ganin yaran sun dawo ga iyayen su.

Batan yara dai ba wani sabon abu ba ne a jihar Kano, yadda aka da?e ana fama da shi, saidai an sha kama wa?anda ake zargi da satar yaran tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Related posts

Leave a Comment