Gwamnatin tarayya ta amince da samar wa da kuma sakin sabon samfurin takardar shaidar zama dan kasa da kuma samar da manhajar waya da za ta saukaka yin rajistar samun lambar NIN.
A cikin wata sanarwa da mai ba Ministan sadarwar kasar shawara kan ayyuka Femi Adeluyi ya fitar a ranar Alhamis, ya ce Ministan, Dr Isah Ibrahim Pantami, ya bayyana matakin a matsayin abun da zai saukaka wa ‘yan kasar hada layukan wayarsu da kuma lambar shaidar zama ‘dan kasar.
Sanarwar ta ce manhajar za ta ba ‘yan Nijeriya da sauran mazauna kasar bisa doka, damar tantance katunansu, ta hanyar waya.
Ta ce kowa zai iya sake sauke takardar shaidar zama ‘dan kasar da aka sabunta ta adireshin hukumar wato dashboard.nimc.gov.ng.
