Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban Dakarun rundunar sojin ?asa, Manjo Janar Farouk Yahaya, ya umarcin sojojin dake ya?i da Boko Haram, ISWAP, da yan bindiga da bsauran masu aikata ta’addanci da kada su sassauta har sai sun yi raga-raga da su baki ?aya sun ga bayansu gaba daya.
Shugaban Dakarun ya bada wannan umarnin ne a sansanin soji dake Mogadishu, Abuja, yayin da ake gudanar da addu’o’i a coci a wurin taron murnar zagayowar ranar sojojin Najeriya 2021.
“Ina ro?on kanmu baki ?aya, kada mu sassauta a yakin da muke, mu cigaba har sai mun ci nasara, mun yi kaca-kaca da yan ta’adda baki ?ayansu a ?asar mu. Mu dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”
“Hakanan ina ro?on junan mu baki ?aya, duk inda muka tsinci kanmu, mu kasance masu ?aukar matakin da ya dace da kuma manufa.” “Idan muna da manufa kuma muka ha?a da addu’a to zamu isa inda muke bu?ata” “Mun samu nasarori da dama a ya?in da muke, saboda haka bai kamata mu sassauta akan aikin mu ba, amma mu ?ora daga nasarorin da muka samu a baya.”
Daraktan gudanar da harkokin addinin kirista, Col. Islongo Mairiga, yayin da yake wa’azi, ya bayyana sojojin Najeriya a matsayin abun alfahari ga ?asar. Ya ?ara da cewa ya kamata sojojin su yi aiki tare da junansu domin samun nasara a kan dukkan ma?iyan zaman lafiya a ?asa.
