Kaduna: Babu Gaskiya A Labarin ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari Da Helikwafta

Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta rahotannin da ke cewa ‘yan fashin daji sun kai hare-hare tare da taimakon wani jirgi mai saukar ungulu.

Tun farko shugaban ?ungiyar tuntu?a ta ‘yan ?abilar Adara da mai magana da yawun ?ungiyar ‘yan Kudancin Kaduna ta SOKAPU sun fa?a cikin wata sanarwa cewa wani jirgin helikwafta ne ya taimaka wa ‘yan fashin dajin yayin hare-haren.

Sai dai cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Kwamashinan Tsaro Samuel Aruwan ya musanta rahoton yana mai cewa jirgin da aka gani na rundunar sojan Najeriya ne da ya kai ?auki wurin.

Kwamashinan ya tabbatar da kashe mutum 31 a garuruwan Dogon Noma da Unguwan Sarki, sannan maharan suka kashe mutum ?aya a Unguwan Maikori tare da ?ona gidaje a ranar Lahadi da ta wuce.

“Zuwan jirgin soja na rundunar Operation Whirl Punch ne ya da?ile yun?urin ‘yan fashin bayan sun kashe mutum ?aya tare da ?ona gidaje. Saboda haka labarin cewa jirgi ya taimaka wa ‘yan fashi ba gaskiya ba ne,” a cewarsa.

Related posts

Leave a Comment