Shugaban Kamfanin ATAR Communication mamallakan Gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty, da Jaridun Muryar ‘Yanci da Voice Of Liberty Alhaji Dr Tijjani Ramalan ya taya mai girma Ministan ya?a labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed murnar nadin Sarautar da masarautar Argungu ta yi mishi na Kakakin Kabin Argugu.
Tijjani Ramalan ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar wadda aka rarraba ta ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Ramalan ya bayyana nadin da masarautar ta Kabin Argungu ?ar?ashin jagorancin mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Mera ta yi wa Lai Mohammed a matsayin abin da ya dace kuma abin a yaba.
Masarautar Kabin Argungu ta yi fiye da shekara dari biyar 5000 da kafuwa tun Zamanin Sarki Muhammadu Kanta 1515.
