Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma Da Sace Matafiya

Miyagun ‘yan bindiga sun kai mummunan farmaki yankin Sabon layi, ?aramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna, sun halaka manona uku. Rahoton jaridar The Nation ya tattaro cewa yan bindigan sun kuma tattara wasu manoma da matafiya sun yi awon gaba da su zuwa cikin dazuka.

Wani shugaban al’umma a yankin, Sallau Ibrahim, ya ce maharan sun shiga ?auyen da misalin ?arfe 12:00 na tsakar ranar Alhamis, 22 ga watan Yuni. “Sun kashe manoma uku, Anas Sabonlayi, Abubakar Dankibiya, da kuma Harisu Unguwar Lemu,”

A cewarsa, yana hasashen wannan harin ?aukar fansa ce kan lugudun wutan da rundunar soji ke ci gaba da yi a yankunan da ‘yan bindigan ke samun mafaka.

Haka nan bayanai sun nuna yan ta’addan sun farmaki matafiyan da suka fito da yammaci zuwa kasuwar Birnin Gwari da nufin cin kasuwar mako-mako ta ranar Alhmis. Sallau ya ?ara da cewa “Sun sace ‘yan kasuwa da matafiya da ke kan hanyar zuwa kasuwa. Mako biyu kenan manoma ba su da sukunin zuwa gonakinsu, yau sun kama hanya ga shi an farmake su.”

Rahoto ya nuna cewa tuni aka yi wa mamatan jana’iza a Sabon Layi da misalin ?arfe 4:30 na yammacin Alhamis kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Haka nan da ake nemi jin ta bakin jami’in hul?a da jama’a na rundunar yan sandan Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce har yanzun bai samu rahoto ba.

Related posts

Leave a Comment