Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ?aramin Ministan makamashin Najeriya, Goddy Jedy Agba, ya bayyanawa yan Najeriya cewa rashin wutan lantarki ya zama tarihi a kasar.
Ministan ya bayyana hakan ne a taron da ma’aikatar labarai da al’adu ta shirya kan nasarorin da Gwamnatin Shugaba Buhari ta samu kan manyan ayyukan cigaban ?asa.
Agba yace nan da karshen shekarar nan, kashi 85% na yan Najeriya zasu samu lantarki yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba.
A cewarsa: “Rashin wutan lantarki ya zama tarihi. Nan da karshen shekara kashi 85% na yan Najeriya zasu samu lantarki.” “Hakazalika dukkan gidaje zasu samu mita – kudin wutan da kaci kadai zaka biya.”
Ya kara da cewa ayyukan lantarki da gwamnatin tarayya ta fara zasu kammala kafin karewar wa’adin shugaba Buhari.
