Da Yiwuwar Wata Rana ‘Yan Bindiga Su Mamaye Fadar Shugaban Kasa – Minista

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rotimi Amaechi, ministan sufuri, ya zargi wasu gurbatattun yan siyasa da kokarin tarwatsa albarkatun ?asa, inda ya kara da cewa hakan yana da hatsari matuka.

A wata hira da ya yi da Jaridar dailytrust, ministan yace shugaban ?asa Buhari, yana yin iyakar abinda zai iya wajen gina ?asar nan kan tubali mai kyau, sai dai cin dudduge da yake samu.

Tsohon gwamnan Rivers na tsawon zango biyu ya bayyana cewa karuwar matsalolin rashin tsaro a ?asar nan ka iya shafar babban birnin tarayyar kasar a kwana a tashi.

“Abinda shugaban kasa yake cewa shine, mu gina muhimman ayyuka a kasa. Shugaban ya kan tambaye mu ya zaka ji idan ka tsinci kanka a Cafe Town? Kunya zaka ji a matsayinka na ?an Najeriya saboda wasu gurbatattu sun kacaccala mana arzikin mu.”

“Yace abu ?aya da zaka ji ana zancen Najeriya shine ya kamata ka kai ziyara Abuja, garin ya ha?u sosai. Amma fa Abuja ba ta ?aukar nauyin kowa, idan bamu yi dagaske ba wataran sai an kore mu daga Abuja.”

“Mutum nawa ne manyan masu fa?a a ji da suka fice daga jihojinsu? Sun tsere sun dawo nan Abuja, saboda ta fi tsaro don shugaban ?asa na ciki. Wata rana wa?annan yaran zasu sami karfin guiwa, su kori kowa su mamaye fadar Shugaban kasa da kafar mu zamu fice.”

Amaechi ya kara da cewa matukaar ba’a dawo kan maganar shugaban ?asa ba, a tabbatar an tattala albarkatun da Allah ya bamu babu shakka muna cikin matsala.

“Idan har bamu bi maganar shugaba Buhari ba cewa kada mu rarraba kan mu kan arzikin da Allah ya bamu kuma mu aiwatar da muhimman ayyuka, to babu bukatar zama tsintsiya ?aya.” “Wasu na cewa masu fafutukar ?allewa sune matsalar mu, ba haka bane; wargajewar tattalin arziki da rashin adalci sune manyan matsalolin mu.”

Related posts

Leave a Comment