Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya umarci ma’aikatar lafiyar jihar da ta gaggauta tura tawagar likitoci domin gudanar da bincike tare da ?aukar matakan da suka dace kan ?ullar cutar masha?o a wasu yankunan jihar
Ma’aikatar lafiyar jihar ta tabbatar da bullar cutar a wasu garuruwan Kafancan da ke yankin ?aramar hukumar Jema’a, bayan bayyanar alamomin cutar a wasu unguwanni a garin na kafancan.
Cikin wata sanarwa da sakataren ya?a labaran gwamnan Muhammad Lawal Shehu ya fitar, ya ce gwamnatin jihar ta ?auki matakin ne bayan samun rahotonnin ?ullar cutar tare da rasa rayuka a garuruwan.
Binciken farko da ma’aikatar lafiyar jihar ta gudanar ya nuna cewa an fara samun ?ullar cutar masha?o a garin na Kafancan tun farkon watan Yuli.
Sanarwar ta kuma ambato gwamnan na yaba wa hukumomin lafiyar jihar bisa ?aukar matakan gaggawa na da?ile ya?uwar cutar, tare da yin kira a gare ta da ta ci gaba da ?o?ari domin ya?ar cutar a fa?in jihar.
A baya-bayan nan cutar masha?o na ci gaba da ?ulla a wasu jihohin ?asar, tare da rahotonnin rasa rayuka masu yawa a wasu jihohin.
Alamomin cutar sun ha?ar da wahalar numfashi, da zazza?i mai zafi, da tari, da kasala, da zafin ma?ogoro da kuma kumburin wuya.
Hukumar lafiyar ta kuma shawarci mazauna jihar da su ?auki matakan kariya domin kaucewa bazuwar cutar a fa?in jihar.
shawarwarin da hukumar ta bayara sun ha?ar da:
- Yawan wanke hannu da sabulu.
- Kauce wa cu?anya da mutanen da suka kamu da cutar
- Rufe baki da hanci a lokacin tari ko atishawa
- Kaurace wa makaranta ko wurin aikin idan ba ka da lafiya
- Yin atisaye ko sassarfa domin inganta garkuwar jiki
- Kai rahoton bullar alamomin cutar
