Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ya kamata Najeriya da makwabtanta da ke yankin tafkin Chadi su ?ara ?aimi wajen sauya dokoki da ayyukan sojin ?asashensu.
Bola Tinubu ya ce sauya dokokin aikin sojin ya zama wajibi sakamakon yadda ?asashen yankin ke fama da ?aruwar tashe-tashen hankula.
Yayin da yake jawabi awajen bikin yayen manyan sojoji kwas na 45 da aka gudanar kwalejin sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna, shugaban kasar ya lissafo wasu kalubalen tsaro da ke fuskantar sojojin ?asar da na sauran ?asashen yankin tafkin Chadi, wa?anda ya ce suna amfani da tsoffin dokokin aikin soji.
Shugaban na Najeriya – wanda ya ?arfafa wa ?asashen Afirka gwiwa wajen yin aiki tare don kawar da kalubale guda da suke fuskanta – ya yaba da irin yunkurin da ?asashen yankin tafkin Chadi ke yi na wanzar da zaman lafiya a yankin.
Ya ?ara da cewa hadin kan da ?asashen yankin tafkin Chadin ke yi wajen yakar ayyukan ‘yan bindiga abin a yaba ne, amma yayi kira da a sauya dokokin domin kawar da barazanar da suke fuskanta
”Dole mu yi kokarin sauya dokokin aikin sojinmu. domin yakar makiyan da ke barazana ga ?asashenmu”.
Dole mu mu sake shiri domin kawar da wannan matsala. Wannan kuma na bukatar sauyi tunani da tsare-tsare da dabarun da amuke amfani da su.
haka kuma shugaba Tinubu ya yi amfani da bikin wajen bayyana manufar tsaro da gwamnatinsa ke son cimmawa, yana mai cewa zai mayar da hankali wajen samar da tsaro da adalci da dimokradiyya da ci gaban ?asar.
