Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar gabannin shirinsa na hana siyar da barasa a wuraren shakatawa a Abuja, masu wuraren shakatawa sun rubutawa ministan babbar birnin tarayya, Bello Mohammed wasika don tunatar da shi batun karar da suka shigar a kansa.
Sun yi kira ga ministan da ya riki doka sannan ya saita hadimansa da kuma dakatar da dokar rufe wuraren shakatawa da karfe 7:00 na yamma a babbar birnin tarayyar.
A wata wasika da ta fito daga lauyan kungiyar, Ifeanyi Remy Agu, gamayyar ta kalubalanci dokar tilastawa masu wuraren shakatawa rufe kasuwancinsu daga karfe 6:00 na yamma a gaban babbar kotun FCT. Don haka sun ja hankalin ministan Abujan kan lamarin bayan samun barazana daga babban mai bashi shawara kan sa ido da tabbatar da bin doka, Kwamrad Ikharo Attah, wanda aikinsa ya yi karo da shari’ar da ke gaban kotun.
A takardar, Agu ya bayyana cewa ya kamata a ce ana rayuwa cike da ‘yanci inda bin doka ke sama da son rai da cin mutuncin jama’a. Ya kuma bayyana cewa don an samu lamarin ta’addanci a daya daga cikin wuraren shakatawar ba yana nufin za a samu hakan a sauran wuraren shakatawa ba da zai kai ga sanya dokar tashi karfe 6:00 na yamma.
